HdM: Matashi mai yankan farce a Gombe | Himma dai Matasa | DW | 20.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

HdM: Matashi mai yankan farce a Gombe

Usman Muhammad wani matashi ne a Gombe da bayan kammala karatunsa ya rungumi sana'ar yankan farce, wacce ba a yi wa kallon sanar wadanda suka yi karatun zamani.

HDM: Gombe Jugend Manikür (M)

Matashi mai sana'ar yankan farce a jihar Gombe da ke Najeriya, Usman Muhammad

Usman Muhammad wanda aka fi sani da "Almakasa," ya shahara a wannan sana'a ta yankan farce wacce ya ce ta masa riga da wando da duk wani rufin asiri da Allah ya ke yi wa dan Adam musamman matashi. Kamar sauran masu sana'ar yankan farcen, Usman Almakasa ya na yawo ne domin yin sana'ar tasa koda yake a kan kira shi a waya ya je har gida ya yi wa iyalai yankan farcen ko kuma ya samu mutum a ofishinsa domin ya gyara masa faratunsa.

Wannan ne ya sa ya samu karbuwa tsakanin al'umma, inda har daga waje mai nisa ko ma wasu garuruwa mutane kan zo domin Almakasa yai musu yankan farce saboda yadda ya lakanci sana'ar da kuma haba-haba da ya ke yi da masu mu'amala da shi. Masu mu'amalada Almakasan dai na yaba yadda ya ke aikinsa musamman cika alkawari da kuma yadda ya zamanantar da ita gami da yadda yake tsabtace kayan sana'ar tasa.

Almakasa ya shaidawa DW cewaz, ya samu nasarori a rayuwarsa saboda wannan sana'a amma wacce yafi tinkaho da ita, ita ce yadda ya koyawa matasa da dama. Koda yake ya gamu da kalubale a lokacin da ya fara sana'ar musamman ganin shi matashi ne mai ilimi ne, sai dai hakan bai sa ya yi kasa a gwiwa ko kuma jikinsa ya mutu ba. Almakasa dai na amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen tunatarwa masu mu'amala da shi lokaci da ranar da ake musu yankan farcen, abin da ya sa ya ke kara samun karbuwa wajen a'umma.

Sauti da bidiyo akan labarin