Matashin ma sana'ar adon daki a Borno
December 2, 2020Sana'ar kawata dakuna da ofisoshi dai wata sana'a ce da yanzu haka ba koawane matashi ne ya ke da tunanin yi ba, saboda ganin yawancin kayayyakin da ake aikin da su kwalaye ne da takardu da aka yi watsi da su da wasunsu ma ake ganin ba su da sauran amfani. To sai dai Muhammad Nasir Umar ya hango haske a wannan sana'a, inda ya ajiye kwalayen takardun shaidar kamala karatunsa ya kuma rungumi wannan sana'ar ka'in da na'in.
Matashin dai ya ce ya yi dogon nazari kafin shigarsa wannan sana'a da ya ce tana rufa masa asiri.
Nasir Umar ya ce matasa maza da mata sun koyi wannan sana'a kuma su na morar ta a halin yanzu. A cewarsa duk kalubalen da ya samu a wannan aiki ya zamar masa nasara, inda kuma ya ke shawarta matasa su zama masu yin sana'a ko mai kankantarta domin akwai rufin asiri a yin sana'o'in hannu. Ya ce tunda ya samu wannan sana'ar aikin gwamnati sai dai ya kalli masu yi.
A cewa Muhammad Nasir wannan sana'a akwai alheri a cikin ta. Jama'a na yin godiya da wannan sana'a saboda yadda ake kyankyare musu dakuna ko ofisoshi musamman, ma Amare da ake aurar da su a irin wanann lokaci. Masu fashin baki kan harkokin yau da kullum dai, na yabawa Nasir saboda a cewarsu bayan yin sana'a da kuma koyawa matasa yana kuma alkinta muhali, abin da yasa su ke ganin da gwamnati ta taimaka masa da hakan ya sanya an jefi tsuntsu biyu da dutse daya wato ga sana'a ga kare muhalli.