HdM: Matashi mai sana′ar jari bola | Himma dai Matasa | DW | 24.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

HdM: Matashi mai sana'ar jari bola

Wani matashi a jihar Katsina da ke Najeriya, ya kama sana'ar sayar da karafuna da aka fi sani da jari bola domin dogaro da kansa. Matashin dai ya bunkasa sana'ar, inda ya yi karatu a jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua da ita.

DW Eco Africa Plastik Recycling

Sana'ar jari bola dai na samun wajen zama musamman a Najeriya

Matashin na hada-hadar sayar da karafunan ne a kasuwar kayan nauyi da ke birnin Katsina, inda ake kai masa karafunan daga bangarori dabam-dabam yana saye. Matashin mai suna  Nura Musa Kofar Kaura ya ce ya samu nasarori sosai a wanann sana'a ta sayar da karafa, inda ya ce ya fara jari bolan da daukar dan buhu yana zagayawa yana sayen karafunan har sana'ar ta bunkasa

Matasa da dama a kasar Hausa kan dogara da aikin gwamnati musamman wadanda suka yi karatun boko, abin da Nura Kofar Kaura ke cewa gurgun tunani ne. Wannan matashi dai yana ci gaba da tasawa saboda yadda sana'ar ta bunkasa, inda yanzu haka yake da shaguna hudu a kasuwar kuma ko da yaushe akwai matasa da ke kewaye da shi.


 

 

Sauti da bidiyo akan labarin