1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

HdM: Matashi da ya kirkiri mota mai sola

March 30, 2022

Wani matashi mai suna Mustapha Abubakar Gajibo da ke zama a Maiduguri ya kirikiri motocin safa masu amfani da hasken ranadon saukaka wa al'umma da kuma muhalli

https://p.dw.com/p/49FhS
Nigeria Jugend Ingenieur Maiduguri
Hoto: Al Amin Muhammad/DW

Mustapha Abubakar Gajibo ya yi zarra tsakanain takwarorinsa matasa inda ya kirkirar motocin da Babura masu tayoyi uku da ke amfani da hasken Rana.

Yanzu haka dai motocin da Babura suna aikin jigilar fasijoji a cikin birnin Maiduguri a farashi mai rahusa.

Mustapha Abubakar Gajibo ya ce ya samu nasarori da dama da ya ke alfahari da su musamman ganin ya na saukaka wa al’umma da kuma alkinta muhalli.