Hawaii: An nemi gafara kan sakonnin hari | Labarai | DW | 14.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hawaii: An nemi gafara kan sakonnin hari

Hukumomin jihar Hawaii da ke kasar Amirka na ci gaba da neman afuwa kan sakonnin gargadin harin makami mai linzami da aka aike ga sama da mutane miliyan guda bisa kuskure.

Wani jami'in hukumar gaggawa ne ya danna madannin da bai shi yakamata a danna ba bisa kuskure, abinda ya haifar da kadawar kararrwa a wayoyin mutanen jihar cewa, " A nemi mafaka a cikin gaggawa". Sakon gaggawa ya haifar da tashin hankali ga mazauna jihar.

sai dai Vern Miyagi wani babban jami'i a hukumar gaggawa ta jihar Hawaii, ya ce "Tabbas abin da ya faru babban kuskure ne ba ganganci ba wanda ya aikata ya yi nadama. Muna ba wa al'umma hakuri, amma wannan kuskuren ba ya nufin a shagala a duk lokacin da za a aike da sanonnin gaggawa na kar-ta kwana."