1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hausawan Chadi na rayu al'adunsu sosai

Mohammad Nasiru Awal MAB
September 11, 2018

Hausawa na Chadi na gudanar da bukukuwa daga lokaci zuwa lokaci don raya al'adunsu na gargajiya, inda suke wasan wuta da kade-kade gami da raye-raye a Ndjamena babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/34fJ0
Nigeria Ramadan
Hoto: picture-alliance/AP Photo/G. Osodi

Hausawan kasar Chadi na gudanar da bukukuwa na al'adun gargajiyar Malam Bahaushe a kokari na hana wadannan al'adu da aka gada kaka da kakkani bacewa. Gidan rediyo da talabijin na Annasur da ke watsa shirye-shiryensa a harsunan al'ummomin Chadi ciki har da Hausa na daga cikin kafafen da ke kokari na daukaka al'adun gargajiyar Hausawa.

 A tsokacin da ya yi dangane da al'adun gargajiyar Hausawa, sarki Hausawan birnin Ndjamena Alhaji Idris Adamou cewa ya yi ko shakka babu a da sun yi sakaci har wasannin gargajiyar na Malam Bahause sun so bacewa a Chadi, amma yanzu kam sun kama wasannin ba kuma za su yarda su sullube musu ba.

'Yan wasan kokuwar gargajiya sun baje kolinsu a bikin raya al'adun gargajiyar Hausawan Chadi a birnin Ndjamena. Sullubawa makida daga Mundu a can kudancin Chadi, ba a barsu a baya ba wajen nuna irin ta su al'adar gargajiyar. Mohamed Ishak Usman da aka fi sani Kalla, mazaunin birnin Ndjamena ne da ba safai yake shiga wasannin raya al'adun gargajiya ba, amma a wannan karon ya baje kolin gadon wasannin wuta da ya yi daga iyayensa.