1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hatsarin Koguna a kasar Kwango

Thomas Klein/Kamalu Sani/ USUFebruary 10, 2016

Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango na daya daga cikin kasashen duniya da kogunan su ke da hadari wanda hakan ke janyo salwantar rayukan 'yan kasar dayawa

https://p.dw.com/p/1HscP
Kongo Boot auf Kongofluss
Hoto: DW/T. Klein

To amma yanzu cibiyar CRFNI da aka samar don bada horo ga matukan jirage na matukar kokarin sauya lamarin. Viviane Peled na daf da zama mace matukiyar jirgin ruwa a Congo River, ta farko da ke karatun ta a makarantar sufurin jiragen ruwa a Kinshasa.

A ko wacce ranar Allah da safe da misalin karfe bakwai daliban na hallara ne a makarantar koyar da nazarin ayyukan sufurin jiragen ruwa a Kinshasa. A yayin da Viviane Peled take a makarantar, tuni har na tsawon shekaru biyu da rabi domin kokarin zama Captain din jirgin ruwan. Kazalika tana daya daga cikin mata hudu da ke wannan gwagwarmayar a ajin su.

"Mata na da mahimmanci ga harkar zirga-zirgar sufurin ruwa. Ina son cewar muddin mace za ta iya shugabantar kasa, to za ta iya jagorantar jirgin ruwa ma ke nan".

Viviane Peled na matukar yin wannan aikin a dai-dai lokacin da jagororin jiragen ruwa wato Captain, basu da yawa a kogunan ruwan Congo. Horaswar dai na bukatar bada kulawa sosai, wannan yana da mahimmanci saboda kogunan kasar Congo, suna matsalolin sosai ga sufuri, kama daga bishiyoyi, yashin bakin gaba wadanda ke kawo cikas ga harkokin sufurin jirgin ruwan.

"Dukkan abinda nake a nan yana da mahimmanci, matasa akasari basa son lissafi, haka kuma abin yake a gare ni, to amma a nan na fahimci cewar irin mahimancin daya ke da shi. Idan zaka tuka jirgi akwai wani abu da ka ke da bukata da shi, wannan kuwa shi ne abun lissafi mai suna Trigonometry. Don haka komai anan yana da mahimmanci wajen tukin jirgin ruwa".

Viviane dai na amfani da lokutan da bata aji wajen ziyartar mahaifiyar ta Marceline, wacce ke kulawa da ita, bayan kanin ta Shilo. Kusan shekaru uku Vivian ta bar Jamhuriyar Afrka ta Tsakiya, kana ta isa Kinshasa, tafiya ce mai hadarin gaske a yayin da ake tafka yakin basasa a kasarta ta haihuwa.

"Baya ga Iyaye na, wannan horaswar tana da mahimmanci a gare ni, saboda na fito ne daga dangin da basu da hali. Nine na yanke shawarar fara karatun tukin jirgin ruwa, daga karshe iyaye na za su amfana da hakan".

Kogunan Congo na da tsawon kilomita dubu 3700, wanda ke zama kasa ta biyar a duniya mai kogunan ruwa masu tsawon.

"Da zaran na kammala karatu na, ina son komawa gida tare da karfafawa 'yan mata gwiwa, don zama Captain iri na"

Viaviane Peled dai bata tsoro a yayin da take kokarin kammala karatun ta a shekaru hudu masu zuwa tare da zamantowa Captain mace ta farko a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Kongo Viviane Peled
Viviane Peled, dalibar koyon tukin jigin ruwaHoto: DW/T. Klein