Hatsarin jirgin ruwa a Italiya ya rutsa da baƙin haure | Labarai | DW | 10.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hatsarin jirgin ruwa a Italiya ya rutsa da baƙin haure

Jami'an agaji sun ce sun ceto mutane kusan ɗari baƙin haure, waɗanda wani jirgin ruwa na kamun kifi da yake ɗauke da su ya nutse dab da gabar tekun ƙasar.

Masu yin bincike sun ce jirgin ruwan wanda ke ɗauke da fasinjoji 120 galibinsu 'yan ƙasar Siriya da suka taso tun makonni biyu da suka wuce daga Siriyar. Sun yi ta sauya jiragen ruwan kafin a ƙarshe hatsarin ya auku wanda a cikin mutane shida suka mutu.

Babban kwamandan jirgin ya ce yawancin waɗanda suka rasa rayukansu mata ne da yara ƙanana waɗanda ba su iya ruwa ba. Kuma ya ce masu yin aikin ninƙaya na ci gaba da yin lallube cikin ruwan tekun domin gano ko akwai wasu gawarwakin mutanen da suka yi saura.

Jama'ar dai na ƙokarin ficewa ne daga Siriya domin guje wa yaƙin basasar ƙasar da ke ƙara yin muni. Wanda a wannan Asabar ƙungiyoyin kare hakkin 'yan Adam na Siriya suka sanar da cewar hare-hare na jiragen saman yaƙi sun yi sanadiyyar mutuwar mutane guda 20 galibi farar hula a garin Latakiya dake a yankin yammanci.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal