Hatsari ya auku a wata mahaƙar ma′adanai a Gini | Labarai | DW | 22.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hatsari ya auku a wata mahaƙar ma'adanai a Gini

masu hakar ma'adanai 12 sun hallaka sanadiyyar zabtarewar ƙasa da ta faru a yankin arewa maso gabashi na ƙasar.

Aƙalla musu haƙar ma'adanai 12 ta hanyar da ta saɓa wa ƙa'ida, suka hallaka yayin da wasu masu yawa suka yi ɓatan dabo sakamakon zabtarewar ƙasa da aka samu cikin yankin arewa maso gabashin ƙasar Gini Conakry. Wasu majiyoyin tsaro da mazauna yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, lamarin ya faru cikin daren ranar Talata da ta gabata a garin Siguiri. Shaidun gani da ido sun ce an ci gaba da gudanar da ayyukan ceto har zuwa wannan Alhamis da ta gabata.Ƙasar ta Gini Conakary da ke yankin yammacin Afirka tana cikin ƙasashen masu ma'adanan ƙarƙashin ƙasa kamar zinare da lu'ulu'u, amma galibin al'ummar ƙasar suna rayuwar hannu-baka hannu-ƙwarya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane