Hassan Mahmud: ′Yan Boko Haram na samun horonsu ne a Somaliya | Labarai | DW | 14.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hassan Mahmud: 'Yan Boko Haram na samun horonsu ne a Somaliya

A dai-dai lokacin da ake kammala taron tsaro na kasa da kasa a birnin Munich na Jamus, Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mahmud ya ce mayakan Boko Haram na samun horo ne a Somaliya.

Shugaban kasar Somaliyan ya kara da cewar mayakan na samun horon ne kafin daga bisani su wuce kai tsaye zuwa kasar da ke a yammacin Afrika.

Ya ce fadawa rikita-rikitar siyasa da cin hanci da hare-haren da kungiyar Al-Shabaab ke kaiwa a kasar babu kakkautawa shi ne musabbabin rashin samun cigaba a kasar.

Kazalika ya kara da cewar rashin samun zaman lafiya a Somaliya, tamkar daukacin yankin yana cikin halin rashin tabbas ne gami da daukacin nahiyar Afrika, a inda ya ce tabbas akwai shaidun da suke nuni da cewar 'yan Boko Haram na samun horonsu ne daga Somaliya.

Shugaban Somaliyan na wadannan kalaman ne a lokacin da ake kokarin kammala babban taron tsaro da jami'an tsaro gami da ministocin harkokin kasashen duniya a birnin Munich a inda mahalarta taron suka tattauna batutuwan tsaro da Siriya da kwararar 'yan gudun hijira.