Harsashin roba ya halaka yaro a Falasdinu | Labarai | DW | 12.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harsashin roba ya halaka yaro a Falasdinu

Falasdinawa 13 ne suka rasu a sakamakon rikicin na Yamma da Kogin Jodan da ya taso tun daga ranar daya ga watannan na Oktoba. A bangare guda kuma wasu da dama sun rasu a Gaza.

Israel Gaza Beschuss Opfer 10.07.2014

Sallar gawar matashin Bafalatsine

Wani yaro Bafalasdine dan shekaru 13 ya rasu bayan harbin da aka yi masa a kansa da harsashin roba, harbin da ya haifar da zubar jini a kwakwalwarsa kamar yadda ma'aikatar lafiya a yankin na Falatsinu ta bayyana.

A cewar ma'aikatar lafiyar ya zuwa yanzu dai Falasdinawa 13 ne suka rasu a sakamakon rikicin na Yamma da Kogin Jodan da ya taso tun daga ranar daya ga watannan na Oktoba. Mafi akasarin wadanda suka rasun dai sun halaka ne sakamakon harbin bindiga yayin da a bangaren Isra'ila ta rasa mutane hudu bayan kai musu farmaki ta hanyar amfani da wuka.

Har ila yau akwai kuma wasu Falasdinawa 11 da suka rasu a Zirin Gaza ciki kuwa har da mace mai ciki da 'yarta me shekaru biyu da suka rasu bayan wani hari da sojan Isra'ila suka kai da jirgin yaki a ranar Lahadi.