1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin siyasa a yankin Palasdinawa

January 2, 2006
https://p.dw.com/p/BvE0

Shugaban yankin Palasdinawa, Mahmud Abbas yayi kurarin soke zabubbukan gama gari da aka shirya gudanarwa a yankin a ranar 25 ga watan nan , matukar mahukuntan Israela ba zasu kyale Palasdinawa dake gabashin birnin Jarussalem kada kuriun su a lokacin zaben ba.

Da alama dai daukar wannan mataki daga bangaren na Mahmud Abbas, ya biyo bayan matsin lambar da yake fuskanta ne daga wasu manya manyan jam´iyyar sa ta Fatah akan wannan batu.

Kasar dai ta Israela a karon farko tace ba zata kyale a gudanar da zabe a gabashin birnin na Jerussalem ba matukar, za a bar kungiyyar Hamas shiga wannan zabe.

Ya zuwa yanzu dai bayanai daga Israela na nuni da cewa tuni mahukuntan kasar suka dawo daga rakiyar matakin da suka dauka, bisa zargi da suke gudu da cewa hakan ka iya kawo tafiyar hawainiya ga harkoki na dimokradiyya a yankin.