1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin yan Tawaye a ƙasar Timor

Tanko Bala, AbdullahiFebruary 11, 2008

Firaministan ƙasar Timor Xanana Gusmao ya tsallake rijiya da baya.

https://p.dw.com/p/D5tv
Firaministan ƙasar Timor Xanana Gusmao ke jawabi ga yan Jarida bayan harin da aka kai masaHoto: picture-alliance/ dpa

Gwamnatin ƙasar Gabashin Timor ta sanya dokar ta ɓaci bayan wani hari da yan tawaye suka kai wanda ya raunata shugaban ƙasar Jose Ramos Horta a wani yunƙuri na neman hallaka shi.

Firaministan ƙasar Xanana Gusmao wanda shi ma ya tsallake rijiya da baya a wata sanarwa da ya bayar, yace dokar ta ɓacin zata cigaba da aiki har kwanaki biyu nan gaba.

Yan tawayen sun kutsa kai har gidan shugaban ƙasar ne a ranar Litinin ɗin nan inda suka yi ta ɗauki ba daɗi da jamián tsaro. Sai dai rahotanni sun ce an harbi shugaban ƙasar a ƙirji da kuma cikin sa. Tuni dai aka hanzarta kai shi zuwa ƙasar Australia inda a yanzu haka ake duba lafiyar sa.

Likitoci a ƙasar ta Austarlia sun ce ko da yake shugaban yana cikin yanayi mai tsanani sakamakon raunukan da ya samu amma akwai alamun sauƙi ga lafiyar ta sa. likitocin suka ce an yi masa ƙarin jini kuma an sanya shi a ƙarƙashin kulawa ta musamman da wasu naurori dake tallafa masa wajen yin numfashi.

A waje guda dai jamián tsaro sun sami nasarar harbe shugaban yan tawayen Manjo Alferdo Reinado wanda dama aka daɗe ana nema ruwa a jallo. A kuma halin da ake ciki ƙasar Australia ta yi alƙawarin tura ƙarin dakarun soji zuwa Gabashin Timon domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro da kare ɓarkewar tarzoma a jaririyar ƙasar ta Nahiyar Asia.

Firaministan ƙasar Xanana Gusmao ya gudanar da taro da jamián Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin tsaro na ƙasar domin ɗaukar matakan da suka dace.