1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Wuerzburg da Ansbach na da hadi da 'yan jihadi

Yusuf BalaJuly 26, 2016

A cewar Mista Herrmann hare-haren na Wuerzburg da Ansbach ta'addanci ne da ba za a kauda idanu a kansu ba.

https://p.dw.com/p/1JW3w
Deutschland Ansbach Explosion PK Joachim Herrmann
Joachim Herrmann ke jawabi ga manema labaraiHoto: Reuters/M. Rehle

Ministan harkokin cikin gida na jihar Bavaria a nan Jamus Joachim Herrmann ya bayyana a ranar Talatan nan cewa hare-haren da aka kai a makon jiya a Wuerzburg ta hanyar amfani da gatari a cikin jirgin kasa da ma wanda ya kai hari da bam a garin Ansbach a ranar Lahadi da ta gabata, hare-hare ne da ke da alaka da masu ikirarin kaifin kishin addinin Islama.

A cewar Mista Herrmann hare-haren na Wuerzburg da Ansbach ta'addanci ne da ba za a yi sakaci a kansa ba, za a sanya idanu sosai a kansa dan kare kara afkuwar hakan a nan gaba.