1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: Hari ya halak sojoji

Lateefa Mustapha Ja'afar
April 28, 2023

Rahotanni daga Burkina Faso na nuni da cewa wasu gun-gun 'yan ta'adda masu tsattsauran ra'ayin addini da ke da'awar jihadi, sun kai hari kan sojoji a gabashin kasar tare da halaka 33 da kuma raunata wasu da dama.

https://p.dw.com/p/4QgKu
Burkina Faso | Ouagadougou | Sojoji | Hari | Ta'addanci
Hare-haren ta'addanci na karuwa a Burkina FasoHoto: picture alliance / ASSOCIATED PRESS

Rundunar sojojin Burkina Fason da ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta bayyana cewa an kai mata harin ne a Alhamis din wannan mako a garin Ouagarou da ke gundumar Gourma. Rundunar da ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, ta kuma kara da cewa sojojin a nasu bangaren sun samu nasarar halaka mayakan masu ikirarin jihadi 40. Tsawon shekaru bakwai ke nan da mayakan masu alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda na al-Qaida da IS, suka addabi Burkina Faso da hare-haren da aka kiyasta sun halaka dubban mutane tare da tilasta kimanin miliyan biyu kauracewa gidajensu.