Harin ta′addanci a masallacin Madina | Labarai | DW | 04.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ta'addanci a masallacin Madina

A kalla mutane uku ne suka hallaka sakamakon harin ta'addanci a birnin Madina a wajen Masallacin Masjid al-Nabawi na Annabi Muhammad (SAAW).

Harin ta'addanci a masallacin Masjid al-Nabawi na Madina

Harin ta'addanci a masallacin Masjid al-Nabawi na Madina

Gidan talabijin din Saudiyan na al-Arabiya ya ruwaito cewa, kawo yanzu mutane uku da suka hadar da dan kunar bakin waken da kuma jami'an tsaro biyu sun hallaka. Wannan dai shi ne hari na uku da aka kai a Saudiyan a wannan Litinin din, inda da sanyin safiya wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a wajen ofishin jakadancin Amirka tare da hallaka kansa da kuma jikkata wasu jami'an tsaro biyu, hari na biyu kuwa an kai shi ne a wajen masallacin birnin Qatif na Muslmi mabiya Shi'a, sai dai maharin ne kawai ya hallaka kuma babu wanda ya samu koda kwarzane.