1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin ta'addanci a Kirkuk da Dibis na Iraki

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 21, 2016

Wasu 'yan kunar bakin wake sun kai hare-hare a sassa daban-daban na birnin Kirkuk da Dibis da ke kasar Iraki.

https://p.dw.com/p/2RVgF
Hare-Haren ta'addanci na ci gaba a Iraki
Hare-Haren ta'addanci na ci gaba a IrakiHoto: picture alliance/dpa/M.Garip

Rahotanni sun nunar da cewa 'yan kunar bakin waken sun kai hare-haren ne a gine-ginen gwamnati da suka hadar da ofishin 'yan sanda da wuraren duba ababen hawa a birnin na Kirkuk, wanda ke karkashin ikon Kurdawa wadanda kuma kawunansu ke a rarrabe. A hannu guda kuma 'yan kunar bakin waken sun kai hari a cibiyar samar da hasken wutar lantarki da wani kamfanin kasar Iran ya gina a birnin Dibis da ke arewacin Irakin. Magajin garin Dibis din Abdullah Nureddin al-Salehiin ya shaidawa kamfanin dillancin Labaran Faransa na AFP cewa 'yan kunar bakin waken sun hallaka ma'aikata 'yan Irakin 12 da kuma Injiniyoyi hudu na kasar Iran. Wadannan hare-hare dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da dakarun na Iraki ke ci gaba da kokarin kwace iko da birnin Mosul daga hannun 'yan ta'addan IS.