Harin sojojin Najeriya a sansanin ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 18.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin sojojin Najeriya a sansanin 'yan gudun hijira

Kungiyar agaji ta Likitoci wato Medecins Sans Frontieres ko kuma Doctors Without Borders ta yi takaici da harin sojojin Najeriya a sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar Borno.

Harin sojojin Najeriya bisa kuskure a sansanin 'yan gudun hijira

Harin sojojin Najeriya bisa kuskure a sansanin 'yan gudun hijira

Harin wanda jirgin yakin sojojin Najeriya ya kai kan wani sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Rann na jihar Borno a yankin Arewa maso Gabashin Tarayyar Najeriyar dai, ya yi sanadiyyar asarar rayukan akalla mutane 50 yayin da wasu sama da 120 suka jikkata. Rundunar sojojin Najeriyar ta ce harin ta nufe shi ne a kan mayakan kungiyar Boko Haram da ke ci gaba da kai hare-haren ta'addanci a yankin, yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana harin da cewa na da na sani ne da aka kai bisa kuskure. Ana nasa bangaren shugaban sashen bayar da agajin gaggawa na kungiyar ta Likitoci na Gari na Kowa Hugues Robert ya bukaci sojojin Najeriya da su dauki matakan kare afkuwar hakan a nan gaba yana mai cewa:

"A ganina abin da ya fi zama abin takaici da kuma rudani shi ne, harin an kai shi ne a tsakiyar yankin da ke a karkashin kulawar sojoji. Akwai rudani na gaske cikin lamarin, muna fatan sojojin za su dauki matakan da suka kamata domin kare afkuwar hakan a nan gaba."

Dubban rayukan da dukiyoyin al'umma ne dai suka salwanta tun bayan barkewar wannan rikici na Boko Haram a Najeriya, wanda daga bisani ya hada da wasu kasashe da ke makwabtaka da ita.

Sauti da bidiyo akan labarin