1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farmakin soja ya halaka mutane a Siriya

Binta Aliyu Zurmi
December 8, 2019

A Siriya mutane 20 sun halaka wasu da dama sun ji rauni sakamakon a jerin hare-hare ta sama da dakarun sojin kasar hadin gwiwa da na Rasha suka kai a yankin Idlib.

https://p.dw.com/p/3UOcj
Syrien Explosion in Qamishli
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Anha

Masu sa ido a kan kare hakkin dan Adam a kasar Siriya ne suka sanar da wannan harin, inda suka kara da cewa harin ya shafi kauyuka biyar ne na yankin Idlib a yayin da jirgin yakin Rasha ya yi luguden wutan kan wata kasuwa da ya yi sanadiyar kashe mutane tara tare da karin wasu hudu a kauyen al-Bara, yara takwas na daga cikin wadanda harin ya rutsa da su. Shugaban Siriya Bashar Al-Assad ya sha alwashin kwato duk yankunan da ke hannun 'yan tawayen kasar.