Harin Saudiyya a Yemen na ci gaba da hallaka fararen hula | NRS-Import | DW | 10.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Harin Saudiyya a Yemen na ci gaba da hallaka fararen hula

Bayan harin da ake zargin rundunar kawancen da Saudiyya ke jagoranta da kaiwa a Yemen da ya hallaka mutane sama da 140 tare da jikkata wasu da dama, Iran na son tura jirgi domin kwaso wadanda suka jikkata.

Kasar Iran da ke goyon bayan 'yan tawayen Huthi a kasar Yemen, ta nemi tallafin Majalisar Dinkin Duniya domin aike wa da jirgi na musamman da zai kwaso mutanen da suka jikkata a mummunan harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 140 yayin da wasu fiye da 525 suka samu ranuka.

Ministan harkokin kasashen ketare na kasar ta Iran Mohammad Javad Zarif ya nuna bacin ransa ga halin rashin imanin da aka nuna a wannan hari da aka kai na ranar Asabar, a dai-dai lokacin da al'umma ke zaman makoki a Sanaa babban birnin kasar ta Yemen da ke hannun 'yan tawayen na Huthi.

Daga nata bengare kasar Kanada ta nemi da a aiwatar da binciken kwakwaf kan wannan hari. Sai dai rundunar kawancen da kasar Saudiyya ke wa jagorancin ta yi watsi da zargin da ake na cewa ita ce ta kai wannan harin.