Harin rundunar kawance ya halaka mutum 26 | Labarai | DW | 01.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin rundunar kawance ya halaka mutum 26

A kasar Yemen akalla mutane 26 ne suka rasa rayukansu a sakamakon wani hari ta sama da ake zargin dakarun rundunar kawance da Saudiya ke jagoranta da kai wa.

Harin ya yi sanadiyar lalata wani Otel inda aka fi samun asarar rayuka, wasu da dama sun rasa rayukansu a sanadiyar harin da ya shafi wata kasuwa da ba ta da nisa daga ginin wannan Otel, lamarin ya auku a yankin Saadah na arewacin kasar, rahotannin na cewa ba a iya tantance adadin wadanda suka sami rauni a sanadiyar harin na wannan Laraba ba kawo lokacin fitar da sanarwar.

Rahotanni na cewa an ga masu aikin jin kai a yayin da suke kokarin kwashe gawarwakin a sakamakon harin. Shekaru fiye da biyu da aka kwashe ana yaki, ya jefa kasar ta Yemen cikin mawuyacin hali da tsananin bukatar taimako.