1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai harin roka a Borno

February 24, 2021

A maraicen ranar Talata ce dai mayakan Boko Haram suka kai wasu hare-haren roka a mabambanta wurare a garin Maiduguri na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Kasar.

https://p.dw.com/p/3pmOm
Mutmaßlicher Boko-Haram-Angriff in Nigeria
Hoto: picture-alliance/AP/Jossy Ola

Mayakan na Boko haram sun yi yunkurin kai hari wasu kauyuka sai dai jami’a tsaro sun dakile kokarin na su abunda ya su ka yi ta harba manyan rokoki cikin birnin da ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutum 10 yayin da wasu 47 su ka jikkata. 

Mutum tara daga cikin wadan da su ka mutu matasa da yara ne da ke wasan kwallon kafa a lokacin da mayakan su ka harbo rokar a unguwar Gwange da ke cikin kwaryar Maiduguri.