Harin Rasha ya kashe mutane 11 a Ukraine | Labarai | DW | 26.01.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin Rasha ya kashe mutane 11 a Ukraine

An sami karin mutanen da suka mutu yayin haren-haren da Rasha ta kaddamar a wasu birane na kasar Ukraine, bayan amincewar kasashen Yamma na kara aike wa Ukraine da mayan tankokin yaki.

Wani birnin Ukraine da aka lalata

Wani birnin Ukraine da aka lalata

Rahotanni da ke fitowa daga Kiev babban birnin kasar na cewa hare-haren sun halaka akalla mutane 11 da jikkata wasu 11 tare kuma da lalata cibiyoyin samar da lantarki da dama a kasar. A cewar kakakin hukamar aikin agaji ta Ukraine, hare-haren masu matukar muni sun shafi birane 11 na kasar, amma sun fi tsanani ne a kusa da birnin Kiev fadar gwamnatin kasar.

Rasha ta zafafa hare-haren ne bayan amincewar kasashen yamma na kara aikewa Ukraine da mayan tankokin yaki, matakin da fadar Kremlen  ta ce tamkar kasashen sun shiga yakin ne gadan-gadan