Harin mayakan Houthi a Yemen ya hallaka fiye da mutane 20 | Labarai | DW | 08.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin mayakan Houthi a Yemen ya hallaka fiye da mutane 20

Wani makaman roka da mayakan Houthi a Yemen suka kai a Aden ya hallaka fiye da mutane 20 sannan da dama sun jikata.

Mutane 22 sun hallaka lokacin da 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen suka harba makaman roka a gidajen mutane a garin Aden, kamar yadda majiyoyin asibiti da jami'ai suka tabbatar. Akwai wasu mutane kimanin 70 da suka samu raunika. Ana zargin mayakan na Houthi da tsageru masu goyon bayan tsohon Shugaba Ali Abdullah Saleh da kai farmakin.

Amirka ta kara himma wajen bai wa kasar Saudiya makamai yayin da take jagorancin kai hare-hare kan mayakan Houthi a Yemen wadanda suke samun tallafi daga kasar Iran.

Saudiya tana barin wuta ta sama inda take iko da sararin samaniyar kasar, domin kare gwamnatin Shugaba Abed Rabbo Mansour Hadi, wadda ke fusktanar tawaye daga mayakan na Houthi. Daruruwan mutane sun mutu yayin da wasu dubbai suka jikata sakamakon rikicin da ke faruwa. Mayakan 'yan tawayen na Houthi sun kame yankin mafi girma a cikin kasar ta Yemen.