Harin kwantan bauna ya kashe sojojin Nijar | Labarai | DW | 21.10.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kwantan bauna ya kashe sojojin Nijar

Majiyoyin gwamnati sun tabbatar da cewa shugaban gundumar Bakilare ya tsira daga harin da maharan suka kai wa ayarinsa, bayan da suka bude wuta kan jami'an tsaro. Sai dai mutane da dama sun jikkata bayan mutuwar wasu.

Harin kwantan bauna kan ayarin shugaban gundumar Bakilare ya yi sanadiyar mutuwar sojoji shida a loakcin da suke kan hanyar tafiya a kan iyakar Nijar da Burkina Faso.

Wannan dai shi ne karon farko da masu tada kayar baya suka kai hari kan wani jami'in gwamnati a yankin, duk da cewa yankin ya sha fuskantar hare-hare na mayakan al-Qaeda da IS a shekarar 2021.

Dama dai yankin Bankilare da ke iyaka da arewacin Burkina Faso na zama yanki mai hatsari na mayakan jihadi da ya hade iyakar kasahsen Mali da Nijar da Burkina Fason. Ko a farkon wannan mako sai da mahara suka kashe jami'an tsaro uku tare da jikkata wasu 7 a wani harin da suka kai ofishin 'yan sandan a yankin Tilaberi.