Harin kuskure ya halaka sojojin Pilipin 10 | Labarai | DW | 01.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kuskure ya halaka sojojin Pilipin 10

Dara ta ci gida a kasar Pilipin, yayin da rundunar sojojin sama na kasar suka kai wani somame bisa kuskure da ya kashe sojojin gwamnati 10 tare da jikkata wasu takwas.

Rundunar tsaron kasar ta Pilipin ta ce harin ya faru ne bisa kuskure a lokacin da jiragen yakin sama ke shirin kaddamar da hari a wani sansanin 'yan ta'adda da ke birnin Marawi a kudancin kasar. Hukumomi tsaro sun ce cikin mayaka da sojojin suka kashe a baya, angano wasu 'yan kasashen Saudiya da Malesiya da Indonesiya da Yemen da kuma jamhuriya Chek.

Dama dai gwamnatin Pilipin na samun goyon bayan dakarun hadin guiwa akalla 30 da ke yakar kungiyar IS wadda ake zargin sun kai 500 a kudancin kasar. A yanzu dai kasar na daukar matakan hana sake faruwar hari bisa kuskure.

A baya dai an sha gwabza kazamin fada tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindiga a kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sojoji 25 tare da halaka 'yan ta'adda da dama tun bayan da shugaba Rodrigo Duterte ya ayyana dokar ta baci a kan 'yan ta'adda.