Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane a Afghanistan | Labarai | DW | 13.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane a Afghanistan

Wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa motar da yake cikinta, a Afghanistan inda ya hallaka mutane a kalla 33 tare da jikkata wasu mutanen 10 a Kudu maso Gabashin kasar.

Harin dai ya wanaka ne kusa da wani ofishin bincike na jami'an tsaro, inda dan kunar bakin waken ya tarwatsa motar da yake ciki mai shake da bama-bamai yayin da dumbun motoci ke tsaye a wurin. A cewar ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya da ke wannan kasa, 12 daga cikin wadanda suka rasun dukanninsu yara kanana ne, inda daga nata bengare rundunar sojan Amirka ta sanar cewa babu ko daya daga cikin ma'aikatanta cikin wadanda suka rasu ko suka jikkata.