Harin kunar bakin wake a Potiskum | Labarai | DW | 05.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Potiskum

Maharin ya dana bam din ne a wani Coci mai suna Redeem Church da safiyar lahadi a garin Potisukum na jihar Yobe inda ya halaka mutane shida.

Wadanda suka shaida al’amarin sun bayyana cewa dan kunar bakin waken wanda aka sauke a babur din nan mai tayoyi uku, wanda aka fi sani da Keke NAPEP ya kutsa cikin Cocin a unguwar Jigawa da ke kan hanyar zuwa Bauchi a garin na Potiskum inda ya tada Bam da ke daure a jikin sa, kuma nan take mutane da ke cikin Cocin a lokacin suka mutu sai wata mace daya ce kawai ta tsira da rauni, wadda ita ma daga baya ta mutu.

Ya zuwa yanzu dai an kwashi gawawakin mamatan zuwa babban asibitin garin Potiskum. Inda 'yanuwan wadanda abin ya shafa suke zuwa tabbatar da ko su ne.

Babu dai wanda ya dauki alhakin kai wannan hari amma a baya Kungiyar Boko Haram ta sha daukar alhakin irin wadan nan hare-hare. A kwanakin nan Kungiyar ta zafa hare-haren zuwa wuraren ibada inda wasu hare-hare da zargin Kungiyar ta kai a wasu kauyukan jihar Borno su ka yi sandiyyar mutuwar mutane da dama.