Harin kunar bakin wake a Masar | Labarai | DW | 24.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Masar

Wani hari da aka kai da mota mai shake da bama-bamai a Masar, yayi sanadiyar rasuwar sojoji 26, yayin da wasu 26 suka jikkata a wannan Juma'ar (24.10.2014).

A cewar jami'an tsaron kasar ta Masar, harin ya faru ne a yankin arewa maso yammacin Al-Arich, yankin dake da tarin duwatsu bayan da matukin motar ya tashi bam din kusa da sojojin. A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta masar ta fitar, tace a ayammacin yau din nan ne shugaba Abdel Fattah al-Sissi, yayi kiran wani taron gaggawa na majalisar tsaron kasar domin bi sau da kafa yadda lamarin yake a wannan yanki inda hadarin ya afku. Wannan dai shine babban hari mai muni da ya rutsa da sojoji masu yawa tun bayan hambare zabeben shugaban kasar Mohamed Morsi a watan Yuli na 2013.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba