1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake a Maiduguri

November 25, 2014

Rahotanni daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno da ke Tarayyar Najeriya na nuni da cewa wani bom ya fashe a babbar kasuwa da ake kira da Monday market wacce take tsakiyar birnin.

https://p.dw.com/p/1Dslg
Hoto: AFP/Getty Images

Ana dai fargabar cewa mutane da dama sun hallaka wasu kuma sun jikkata sakamakon harin. Shaidun gani da ido sun ce da safiyar Talatar nan ne bom din ya fashe a wani yanki na kasuwar da ke da cunkoson jama'a musamman ma leburori masu aikin sauke kaya a kasuwar ta Monday Market. Wakilinmu na Gombe Al-Amin Suleiman Muhammad ya ruwaito cewa kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, haka nan ma jami'an tsaro basu ce komai a kai ba saidai sun killace wurin da abin ya afku, inda ake tantance gawarwakin wadanda tashin bom din ya rutsa da su. Saidai Abba Aji Kalli shugaban kungiyar tsaron hadin gwiwa ta farrar hula da aka fi sani da Civilian JTF ta jihar Bornon, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce akallah mutane 30 ne suka rasa rayukansu bayan da 'yan harin kunar bakin waken sanye da dogayen hijabai suka tada bama-baman da ke jikinsu a tsakiyar cunkoson jama'a. Tuni dai ‘yan kasuwa suka rufe shagunan su don gudun abinda ka iya biyo baya.

Mawallafii: Al-Amin Suleiman Muhammad/Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu