Harin kunar bakin wake a Kabul | Labarai | DW | 06.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Kabul

Wani dan kunar bakin wake ya kaiwa ayarin dakarun Amurka hari a birin Kabul din kasar Afganistan ya kashe akalla mutane 5,tare da raunana wasu mutane 7,acewar jami’an kasar.A harin daya auku da safiyar ta yau dai, an lalata motocin sojojin Amurkan guda biyu da wasu biyu na farar hula.Bugu da kari harin ya lalata wasu shaguna masu yawan gaske.Ministan kula da lafiya na Afganistan Amin Fatemi,ya shaidar dacewa wasu fararen hula hudu ne suka rasa ransu,ayayinda wasu mutane 7 da suka hadar da mace guda da karamin yaro suka jikkata.Rahotannin gidan talabijin na kasar dai ya nunar dacewa,akwai sojin Amurka guda daya rasa ransa,inda suka nuna abunda ya rage na gawarsa.Harin wanda ya auku a wani titi da ake yawaita kai hari,ya kuma raunana dakarun Amurkan.