1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Izraeal ya kashe Kwamandan Hamas

November 14, 2012

Kwamandan rundunar tsaron Hamas Ahmed Jaabari na daga cikin mutane shida da hare haren jiragen yaƙin Izraela ya kashe a zirin Gaza

https://p.dw.com/p/16jPA
Hoto: Reuters

Palastinawa guda shida da suka haɗar da wani kwamandan rundunar tsaron Hamas Ahmed Jaabari ne , hare haren jiragen yaƙin Izraela a zirin Gaza ya kashe a wannan larabar. Sanarwar ma'aikatar harkokin cikin gida na gwamnatin Hamas dake Gaza na nuni da cewar, sojojin izraela sun kai hare hare guda 20 da jiragen yaƙi akan wasu yankunan palastinu da suka hadar da headquatan 'yan sanda, kamar yadda kakakin gwamnati Islam Shahwa ya shaidar. Ya kara da cewar a kalla wasu mutane 25 sun samu raunuka, a wannan harin daya fara tun daga karfe huɗu na yammaci. Shima likitan dake asibitin Shifa a birnin Gaza Ayman Sahabani ya tabbatar da mutuwar commandan sojin na Hamas Ahmed Jaabari. Tuni dai hukumar leken asirin Izraela ta Shin Bet da rundunar tsaron ƙasar ta Bani yahudu suka tabbatar da kai harin. Izraelan dai ta ce Jaabari ne keda alhakin shirya dukkan hare haren ta'addanci a yankin.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal