Harin Isra'ila ya kashe gomman mutane a Gaza
September 21, 2025
Talla
Ma'aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta ce, a kalla Falasdinawa 31 ne suka rasa rayukansu a wani harin da Isra'ila ta kai kan wasu gidaje a Zirin. Mutane da dama ne ke tserewa yayin da tankokin yakin Isra'ila ke kara matsawa kusa da garuruwan da ke dauke da jama'a.
Karin bayani: Isra'ila na ci gaba da rushe gidaje a Gaza
Isra'ila dai ta ce Gaza ce babbar matattarar maboyar Kungiyar Hamas, inda tun bayan zafafa farmakinta a farkon wannan watan, rundunar sojin kasar ta ke lalata ayarin gidaje da ta yi ikrarin mayakan Hamas na amfaani da su. Rundunar sojin Isra'ila dai bata ce komai dangane da mutuwar fararen hular ba, sai dai a cewarta, dakarunta sun kashe mayaka da dama.