Harin Isra′ila ya hallaka ′yan Hezbollah | Labarai | DW | 19.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin Isra'ila ya hallaka 'yan Hezbollah

Wasu hare-hare da Isra'ila ta kai a tuddan Golan sun yi sanadin rasuwar wasu mayakan kungiyar Hezbollah ciki kuwa har da dan guda daga cikin manyan kwamandojin kungiyar.

Wata majiya ta jami'an tsaron Isra'ila ta ce mayakan na Hezbollah sun gamu da ajalinsu ne sanadiyyar hare-hare na roka da aka kai musu daura da Quneitra da ke bangaren Siriya na yankin na tuddan na Golan.

A wata sanarwa da ta fidda kungiyar ta Hezbollah ta tabbatar da rasuwan mayakanta shidda ciki kuwa har da Mohammed Issa wani babban kwamandanta da ke kula da aiyyukan kungiyar a kasashen Siriya da Iraki.