1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

120309 Amoklauf Winnenden

March 12, 2009

An fara neman dalilan da suka sanya kai hari na kan mai uwa da wabi a garin Winnenden

https://p.dw.com/p/HAXs
Makoki a Winennden bayan hari akan makarantar sakandareHoto: AP

Wai shin mai ya sa haka ta faru? Wannan dai ita ce tambayar da har izuwa sanyin safiyar yau Alhamis ɗaukacin Jamusawa ke yiwa kansu musamman a garin Winnenden inda a jiya Larabawa wani matashi ɗan shekaru 17 ya afkawa wata makarantar sakandare, inda yayiwa ɗalibai da yawa kisan gilla.

´Yan wannan makarantar sakandare dake a garin Winnenden dake jihar Baden-Württemberg a kudancin Jamus, a yau sun yi gangami a tsakiyar kyadura da aka kunna a gaban makarantar suna riƙe da kwalaye da takardu da suka rubuta tambayar shin mai ya sa haka ta faru? Wannan dai wani lokaci ne na alhini a wannan ɗan ƙaramin gari inda yanzu haka ´yan jarida da wakilan tashoshin telebijin bila-adadin suka kakkafa sansanoninsu a daidai lokacin da ake zaman makoki da juyayi dangane da abin da ya farun a jiya Laraba. Wata mata da ta je ajije kyandur ɗin ta a gaban makarantar ta bayyana hali na kaɗuwa da har yanzu take ciki.

Amoklauf Winnenden
Masu kunnan kyandur a wajen harabar makarantar AlbertvilleHoto: AP

"Ina cikin matuƙar baƙin ciki. Kuma ban san irin kalaman da ya kamata in yi amfani da su ba don nuna baƙin cikina. Kamar sauran iyayen yara ni ma fata ne shi ne yara na su kasance a raye kuma cikin ƙoshin lafiya. Ina miƙa ta´aziyata ga dukkan iyayen yaran da wannan ta´asa ta rutsa da su."

Babu wani mai tunanin shiga aji yau a wannan makarantar. Domin a halin da ake ciki masana ilimin halaiyar bil Adam ne ke kula da ɗaliban wannan makaranta a wani gini dake daura da makarantar. Ban da waɗannan masana da suka fito daga wasu jihohin Jamus da ma garin na Winnenden akwai kuma ma´aikatan agajin gaggawa na ƙungiyar Red Cross da su ma suke taimakawa ´yan makarantar. Anette Kohl ma´aikaciyar agaji ce ta Red Cross ta ce suna sa rai a yau kaɗai za su kula da ´yan makaranta fiye da ɗari ɗaya.

"Muna taimakawa juna mu kuma ina fata za mu samu ƙarfin jurewa wannan abu da ya faru. Muna tsammanin dai ´yan makaranta kimanin 150 za su zo nan yayin da wasu za su yi zamansu a gida. A yau dai kam ba za a shiga aji ba, muna jiran ganin yadda abubuwa za su kasance."

Amoklauf in Winnenden Baden Wuerttemberg
Ɗaliban makaranta dake buƙatar taimakoHoto: AP

Harbe harben na kan mai uwa da wabi da yayi sanadiyar mutuwar mutane 16 a garin na Winnenden ba shi ne na farko da wani ɗalibi ya aikata a nan Jamus ba. Alal misali a watan Afrilun shekara ta 2002 wani ɗan shekara 19 ya halaka mutane da dama a harin da ya kai kanw ata makaranta dake garin Erfurt. Sannan a watan Nuwamban shekarar 2006 wani ɗan shekara 18 ya aikata irin wannan ta´asa a tsohuwar makarantarsa dake garin Emsdetten.

Wannan abin na ci-gaba faruwa duk da tsaurara dokar mallakar makamai da hukumomin wannan ƙasa suka yi. Yanzu haka wannan abin da ya sake faruwa ya janyo wata sabuwar muhauwara a ƙasar kan inganta matakan rigakafi don hana irin wannan mummunan zubar da jini sake aukuwa. ´Yan siyasa da hukumomin ƙasar sun nuna buƙatar faɗaɗa aikin masu ba da shawara a fannin halaiyar ɗan Adam a makarantun faɗin tarayyar ta Jamus.

Mawallafi: Knut Bauer/Mohammad Awal

Edita: Umaru Aliyu