Harin bom a masallacin ′yan shi′a a Saudiyya | Labarai | DW | 29.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bom a masallacin 'yan shi'a a Saudiyya

Mutane ukku sun mutu a cikin wani harin kunar bakin wake a masallacin birnin Dammam na kasar Saudiyya da kungiyar IS ta yi ikrarin kaiwa

A kasar Saudiyya hukumomi sun tabbatar da mutuwar akalla mutun ukku a yayin da wasu hudu suka ji rauni a cikin wani harin kunar bakin wake da wani mutun ya kai a wani masallacin musulmi mabiya mazhabin Shi'a a Birnin Dammam na kasar .Wani mutun da lamarin ya faru a gabansa ya ce dan kunar bakin waken ya tayar da Bom din nasa ne a gurin ajiyar motoci lokacin da masu gadin masallacin suka yi kokarin hanashi shiga bangaran da mata ke zama a cikin masallacin.

Tuni dai kungiyar mayakan 'yan jihadi ta IS ta dauki alhakin kai wannan hari.Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin mako daya da kungiyar ta IS ke kai hari a masallacin mabiya mazahabin Shi'a a kasar ta Saudiyya.Mutane 21 ne dai suka mutu a yayin da wasu sama da dari suka jikkata lokacin wani harin da kungiyar ta IS ta kai a masallacin mabiya mazhabin Shi'ar a makon da ya gabata .