Harin Boko Haram ya halaka mutane da dama
September 8, 2018Rahotanni na cewa mayakan sun afka wa mazauna garin da ke a yankin Guzamala sanye da kayan sarki na sojoji inda suka bude wuta kan mazauna yankin dama sojojin da ke a bakin aikinsu. Jami'an tsaro da sauran al'umma sun tsere wa barin wuta a harin na ba-zata daga mayakan.
Wani ganau ya ce fararen hula da dama sun mutu kuma ba zai iya kayyade iyakacin jama'ar da suka rasa rayukansu daga harin na ranar Jumma'a ba, Dubban mutane ne suka kaurace wa gidajensu tun bayan aukuwar harin. Kawo yanzu babu karin bayani daga bakin mahukuntan kasar kan wannan harin.
A watan Yunin da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta umarci dubban 'yan gudun hijira na yankin Gudumbalin da suka tsere wa rikicin ta'addanci da su koma gidajensu bayan da ta ce an shawo kan Boko Haram. Yankin da ke a jihar Borno a Arewa maso gabashin Najeriya ya fuskanci munanan hare-hare inda aka tafka asarar rayuka da dukiya a sanadiyyar ayyukan kungiyar ta Boko Haram.