Harin Boko Haram ya hallaka ′yan banga | Labarai | DW | 22.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin Boko Haram ya hallaka 'yan banga

Mayakan Boko Haram sun hallaka 'yan banga su shida da ke tallafawa jami'an tsaron Najeriya a yakin da suke da masu ta da kayar baya a yankin Arewa maso gabashin kasar.

Civilian JTF (picture-alliance/AP/Abdulkareem Haruna)

Matasa 'yan banga a Najeriya

Hakan ya faru ne sakamakon wasu jerin hare-hare guda biyu da 'yan bindigar suka kai a yankin, kamar yadda 'yan banga suka sanar wa kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP. 'Yan kungiyar ta Boko Haram sun kashe 'yan banga hudu, tare kuma da sace wasu biyu daga cikinsu a wajen birnin Maiguri a ranar Asabar a lokacin da 'yan bangar suke sintiri kusa da sansanin 'yan gudun hijira na Dolori.

Wani daga cikin 'yan bangar ya sanar da cewa mayakan sun zo ne bisa babura, inda suka fada wa 'yan bangar, tare da sace shida daga cikin su, wadanda daga bisani aka tsinci gawawakinsu a dajin, kuma hudu daga cikinsu an yi musu yankan rago ne, sannan wasu 'yan bangar biyu sun mutu ne sakamakon harin kunar bakin wake da wasu mata biyu suka kai a garin Konduga daf da inda 'yan bangan ke ayyukan su na tsaro a cewar majiya ta 'yan bangan.