Harin bama-bamai a Masar | Labarai | DW | 05.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bama-bamai a Masar

Ministan cikin gida na ƙasar Ibrahim Muhammed ya ƙetare rijiya da baya a wani harin bam wanda aka kai a kan ayerin motocin da ke yi masa rakiya.

Wani babban jami'in gwamnatin ya ce wasu mutane ne guda biyu suka dasa bam ɗin a cikin wata motar da ta tashi daf da lokacin da motocin ke wucewa, wanɗanda ya ce jami'an tsaro sun harbe su har lahira.

Majiyoyi na jami'an kiwon lafiya sun ce mutane 25 suka samu raunika yawancinsu jami'an tsaro da kuma farar hula. Jum kaɗan bayan harin a wata sanarwa da ya bayyana ministan na cikin gida ya yi Allah wadai da harin wanda ya kira na kasashi, yazuwa yanzu dai ba a da masaniya dangane da waɗanda ke da alhakin kai harin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe