Harin bama-bamai a Chadi | Labarai | DW | 15.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bama-bamai a Chadi

Rahotanni daga kasar Chadi na nuni da cewa wasu tagwayen bama-bamai sun tashi a N'Djamena babban birnin kasar.

Harin ta'addanci a Chadi

Harin ta'addanci a Chadi

Bama-baman da suka tashi da misalin karfe 10 na safiyar wannan Litinin din, guda ya tashi ne a babbar shelkwatar 'yan sanda da ke kusa da fadar Shugaba Idriss Deby Itno, yayin da gudan kuma ya tashi a wata cibiyar horar da 'yan sanda da ke dab da wani babban asibitin da aka fi sani da asibitin 'yan China. Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai hare-haren, ko da yake ana danganta su da irin harin da 'yan kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a Najeriya suka saba kaiwa. Wakilinmu na N'Djamena Abdourrazak Garba Babani ya ruwaito cewar babu masaniya a kan adadin mutanen da suka rasa rayukansu, sai dai mutane da dama da suka hadar da jami'an 'yan sanda da fararen hula sun hallaka yayin wannan hari.