Harin bam ya yi sanadiyyar rayuka a Borno | Labarai | DW | 01.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya yi sanadiyyar rayuka a Borno

Bam din ya fashe ne a kusa da wata kasuwa mai cunkoson jama'a da ke tsakiyar garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Wata Zara Mustapha wadda ta ganewa idanunta tashin bam din a cikin wata motar gawayi, ta ce mutane sun ranta domin tserewa da rayukansu, da jiki duk jini daga wadanda suka jikkata da wadanda suka rasa rayukansu.

Har yanzu dai babu cikakkaken bayani dangane da yawan mutanen da suka rasa rayukansu, sai dai rahotanni sun ce akwai gawarwarwaki masu yawa da aka tafi da su asibiti. Ana dai danganta harin da ke zuwa cikin wata mai tsarki na Ramadan, da aika aikan 'yan kungiyar nan ta Boko Haram da suka saba kai makamancinsa.

A wani labarin kuma rundunar sojin Najeriya ta sanar da kame wa ni dan kasuwa Babuji Ya'ari da ake zargi da hannu a sace ‘yan mata nan sama da 200 na makaratar sakandare da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka sace a garin Chibok a jihar ta Borno. Kame dan kasuwar ya biyo bayan somame ne da rundunar sojin suka kai. Ana zargin dan kasuwar kazalika da hannu a kisan da aka yi wa sarkin Gwozo, da wasu hare haren Bam a Borno.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu