Harin bam ya ritsa da asibitin Mata a Siriya | Labarai | DW | 29.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya ritsa da asibitin Mata a Siriya

Jiragen yaki sun kai hari a asibitin Mata da ke Lardin Idlib a arewa maso kudancin Siriya.

Wani harin bam da jiragen yaki suka kai a lardin Idlib da ke arewa maso kudancin Siriya ya tarwatsa wani asibitin mata da kungiyar kula da kananan yara ta Save the Children ke kula da shi.

Kungiyar ta Save the Children dai ta yi kira ga dukkanin bangarorin da rikici da juna da su kai zuciya nesa don samun kai dauki ga dubban al'umma da ke cikin yanayi na bukata kana ta bukaci da kauracewa lalata gine-gine masu muhimmaci ciki kuwa har da asibitoci.

Kawo yanzu dai ba a kai ga tantance adadin asarar rayuka da aka samu ba, to amma a cewar kungiyar Syrian Obsarvatory for Human Rights da ke sa ido kan abubuwan da ke faruwa a kasar ta ce harin ya yi sanadiyar rasuwar mutane da dama.

Kungiyo kare hakkin bil'adama da ke Siriya, sun tabbatar da bayanai da ke cewa, dama an kai harin ne da nufin farautar wani dan jihadi da ya ziyarci matarsa da ta haihu a asibitin inda kuma aka hallaka shi.