Harin bam ya kashe mutane huɗu a Jos | Labarai | DW | 25.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya kashe mutane huɗu a Jos

An ba da rahoton cewar an sake samun tashi bam a birnin Jos fadar gwamnatin jihar Filato da ke a Najeriya wanda a ciki mutane guda huɗu suka mutu.

Masu aiko da rahotannin sun ce mutumin da ya kai harin ya samami wasu jama'ar ne da ke kalon wasannin ƙwalon ƙafa na gasar nahiyar Turai.

Maharin ya matso da motarsa a kusa da tarin jama'ar, to sai dai bam ɗin ya fashe kafin ya isa a wurinsu. Wannan harin bam dai na zuwa ne kwanaki 4 da tashin wasu tagwayen bama-bamai a garin na Jos, waɗanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 200.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe