Harin bam ya hallaka sojojin kasar Yemen | Labarai | DW | 19.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya hallaka sojojin kasar Yemen

Akalla sojojin kasar Yemen guda uku sun rasu, wasu kuma guda biyar suka ji rauni a wannan Jumma'a sakamakon wani harin bam da 'yan kungiyar Al-Qaida suka kai.

Wannan dai shi ne hari irin sa na biyu cikin kwanaki uku da aka kai a yankin na Hadramout da ke kudu maso gabashin kasar ta Yemen a cewar wata majiya ta soja. An dai dana bam din ne kuma aka tasheshi daga nesa, yayin da motar sojojin da ke ficewa ta iso daidai wurin a tsakiyar birnin Seyoun, da ke a matsayin birni na biyu a wannan yanki inda 'yan kungiyar ta Al-Qaida ke da yawan gaske.

Sojojin kasar ta Yemen dai na yawan fuskantar matsalolin hare-haren 'yan ta'adda da ake dora alhakinsa a kan 'yan kungiyar Al-Qaida, A ranar Laraba ma da ta gabata ma dai, akalla wasu sojojin guda uku ne suka rasu sakamakon a wani harin a yammacin birnin na Seyoun.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadaou Awal Balarabe