Harin bam ya hallaka mutane 40 a Jimeta | Labarai | DW | 05.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya hallaka mutane 40 a Jimeta

Harin ya wakana ne a wata kasuwar da ke da cunkoson jam'a a garin na Jimeta, lamarin da ke ya haifar da fargabar yiwuwar samun mutanen da suka mutu a nan gaba.

A tarayyar Najeriya akalla mutane 40 suka hallaka a yammacin jiya Alhamis a sakamakon tashin bam a tsakiyar wata kasuwar birnin Jimeta fadar Jihar Adamawa a yankin Arewa masu gabashin kasar.

Bam din dai ya tashi dab da inda cunkoson jama'a ya ke yayin harkokin kasuwa da zirga-zirgar jama'a a bakin kasuwar, lamarin da ya haddasa mutuwar mutanen dama jikkatar wasu masu yawan gaske. Ana kuma fargabar karuwar salwantar rayuka.

Tuni dai Gwamnan jihar ta Adamawa Muhammad Umaru Jibrilla, ya bayyana kaduwa game da wannan lamarin da ke zama karon farko a jihar, kuma kwanaki kalilan da hawansa karaga.

Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari .Sai dai harin na kama da irin wanda kungiyar Boko Haram ta saba kaiwa a wannan yanki na Arewa maso gabashin kasar ta Najeriya.