Harin bam ya hallaka da dama a Kano | Labarai | DW | 24.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya hallaka da dama a Kano

Jim kadan bayan fashewar bam a wata tashar mota a Potiskum, wasu masu kunar bakin wake biyu sun sake tayar da wasu bama-baman a kano

A kalla mutane 15 ne suka rasa ransu wasu kuma da dama suka jikkata sakamakon harin bam da aka kai tashar motar kano line dake birnin Kano. Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewar da yammacin yau ne aka jiyo karar fashewar bam din lokacin da ake tsakar yin lodi a tashar. Wasu da abin ya faru a kan idonsu sun bayyana cewar motoci 4 ne suka kone a tashar ciki kuwa hadda wacce aka cika ta da fasinjoji.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano Ibrahim K. Idris ya ziyarci wurin jim kadan bayan fashewar bam din ya kuma bayyana cewar zasu yi bincike domin gano masu hannu cikin wannan hari.

A wannan talatar wannan ne karo na biyu da bam ke fashewa, inda sao'i hudu kafin fashewar bam din wani mutumi ya shiga wata motar da ke lodi a tashar dan Borno da ke Potiskum a jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabashin kasar.