Harin Bam ya halaka rayuka a Maiduguri | Labarai | DW | 17.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin Bam ya halaka rayuka a Maiduguri

Rahotannin da ke fitowa daga birnin Maiduguri a Najeriya, na cewa wata 'yar kunar bakin wake ta halaka mutane takwas tare da jikkata wasu 15 da asubahin wannan Litinin.

Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Borno Ahmed Satomi wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce 'yar kunar bakin waken ta tayar da Bam din da ke jikinta ne a wani masallaci da ke yankin 'London Ciki' da ke Maiduguri.

Da ma dai sai da wasu suka sa yarinyar gaba daga wata unguwar lokacin da suka fuskanci take takenta, sannan ta isa yankin na London Ciki ta kuma aikata ta'asar.

Gabanin tayar da Bam din dai, sai da 'yan kato-da-gora suka yi kokarin dakatar da ita lokacin da ta doshi masallacin, amma fa sai ta kutsa da karfi ta kuma tayar.

Bayanai sun kuma ce an ma kama wasu matan dauke da nakiyoyin su uku a Maidugurin da jijjifin safiyar ranar ta Litinin.