Harin bam ya halaka mutane da dama a Damaturu jihar Yobe Najeriya | Labarai | DW | 07.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya halaka mutane da dama a Damaturu jihar Yobe Najeriya

Da fari dai an tattara fulani ne da nufin za a yi musu wa'azi sai kawai aka ji tashin bam a tsakaninsu, abin da ya raunata da halaka mutane.

Rahotannin da ke fitowa daga Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe Arewa maso Gabashin Najeriya na nuna cewa mutane da dama sun mutu wasu kuma sun jikkata bayan tashin wani bam da ake zaton na kunar bakin wake ne da wasu da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka kai.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun tara wasu Fulani da nufin yi musu wa'azi inda aka tada bam din tsakaninsu wanda ya hallaka mutane ciki har da mata da yara.Wasu dai rahotanni na nuni da cewa sama da mutane 15 ne suka rasa rayukansu. Ya zuwa yanzu dai babu bayanai da hukumomi suka fitar kan wannan sabon hari.