Harin bam a Najeriya da Jamhuriyar Kamaru | Labarai | DW | 28.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam a Najeriya da Jamhuriyar Kamaru

Wasu mahara da ba a tantance ko su waye ba sun kai harin kunar bakin wake a birnin Maiduguri na Najeriya da Lardin Arewa Mai Nisa na Jamhuriyar Kamaru.

Kimanin mutane 20 aka bada labarin rasuwarsu sakamakon wani harin bam da aka kai kan wani masallaci a birnin Maiduguri na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wani jami'an hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA Mohammed Kanar da ke aiki a jihar ta Borno kuma ya shaida faruwar harin ya ce baya ga wanda suka rasu, akalla mutane 91 sun jikkata.

Can ma a Jamhuriyar Kamaru, harin ne na kuna bakin wake aka ki inda wasu 'yan mata biyu suka tada bam din da ke jikinsu a Lardin Arewa Mai Nisa gab da mashigar wata kasuwa. Jami'an tsaro a yankin da lamarin ya faru suka ce harin bai yi sanadiyar rasuwa kowa ba ban baya ga matan, amma wani dan kato da gora guda ya jikkata.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dau alhakin kai hare-haren wadannan wurare biyu a Najeriya da kuma Kamaru amma kungiyar nan ta Boko Haram ta sha kai hare-hare makamantan wadannan a kasashen biyu.