Harin al-Shabab a Kenya ya hallaka mutane kimanin 70 | Siyasa | DW | 22.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Harin al-Shabab a Kenya ya hallaka mutane kimanin 70

Kungiyar 'yan kishin addini ta al-Shabab wadda ta kai harin a kan wata cibiyar kasuwanci da ke birnin Nairobi ta ce hukumomin Kenya ba za su iya cin lagwansu ba.

Sojojin kasar Kenya na ci gaba da yi wa 'yan bindigar Musulmi dake garkuwa da mutane a wata cibiyar kasuwancin dake birnin Nairobin, inda aka kashe akalla mutane kimanin 70 a wani hari da kungiyar al-Shabab mai adawa da shigar sojojin Kenya a rundunar kiyaye zaman lafiya a Somaliya, ta kai. Yayin da Isra'ila ta ce jami'anta na taimaka wa takwarorinsu na Kenya don kubutar da mutane da 'yan Al-Shabab suka yi garkuwa da su.

Jiragen sama masu saukar ungulu na ci gaba da shawagi a saman cibiyar kasuwancin ta Westgate dake babban birnin na Kenya da ke da manyan shaguna mallakin Isra'ila inda kuma baki da masu hannu da shuni na Kenya ke yawaita ziyarta.

Taimako daga ketare

Kamfannin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewar tallafin da jami'an Isra'ila ta kai ya taimaka wajen ci gaba da kubutar da mutane daga harabar cibiyar kasuwancin. Sai dai rahotanni na cewar har yanzu akwai kimanin mutane 30 da 'yan tarzomar ke rike da su.

Wani wakilin kamfanin dillancin labaran Reuters dake kusa da cibiyar, ya ce an yi wata musayawar wuta ta kimanin rabin minti wadda ta kawo karshen kiki-kakar awowi da dama.

A daura da wannan kuma, rundunar sojin kasar ta Kenya ta ce ta kara yawan sojinta kuma sun yi wa cibiyar kasuwancin kawanya yayin da wasu sojin da dama suma suka kutsa kai cikin ginin da nufin kawo karshen garkuwar. Sai dai Mutea Iringo dake zama sakataren kasa a ma'aikatar cikin gidan Kenya ya ce sojojin suna sara suna duban bakin gatarinsu.

"Gwamnati ba ta yi sako-sako ba, ta girke karin dakaru ciki har da sojoji na musamman a yankin, baya ga haka mun kuma sojoji sama na sanya ido a kan abubuan da ke faruwa."

Karan harbi nan da can

An yi ta jin karan harbe-harbe jefi jefi, kuma ba a tantance yawan mutanen da 'yan bindigar ke ci gaba da garkuwa da su ba. Daga cikin wadanda suka kubuta kawo yanzu har da wannan matar, wadda ake ba ta magani a cikin motar daukar marasa lafiya.

"An harbe kwastamomi da ma'aikata da yawa. Na tsaya dab da wani mutum da aka kashe shi."

'Yan Kenya masu hannu da shuni da kuma baki ke yawaita zuwa cibiyar kasuwancin ta Westgate, musamman a karshen mako lokacin da mutane da yawa ke zuwa sayayya ko zama wuraren shan gahawa da kuma gidajen abinci. Alkalumman da gwamnatin Kenya ta bayar baya-bayan nan na cewa mutane kimanin 60 suka rasu sannan fyie da 150 sun jikkata. Shugaba Uhuru Kenyatta wanda wannan lamarin ke wani kaulabalen tsaro na farko da ya fuskanta tun bayan zaben watan Maris ya ce wasu danginsa na daga cikin wadanda suka rasu: Bayan jaje da ya yi wa dukkan iyalan da suka rasa 'yan uwa a harin ya sha alwashin sannan a hannu .

"Ina mai nuna wa karara cewa za mu zakulo 'yan bindiga daga maboyarsu. Za mu hukunta su game da wannan ta'asar da suka aikata."

A halin da ake ciki mataimakin shugaban Kenya, William Ruto ya bukaci da a dage shari'ar da ake masa a kotun ICC da ke birnin The Hague don komawa gida ya dafa wa shugaban.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin